ABNA24 : Har ila yau shugaban kasar ta Iran ya bukaci da a kafa kwamiti-kwamiti a yankunan da aka bai wa launin ja da ruwan goro, domin sanya idanu akan yadda ake aiki da matakan dakile cutar ta mashako, Covid-19.
Shugaban na kasar Iran ya yi ishara da cewa da akwai gundumomi 18 a Iran da suke cikin yanayin da bai dace ba wajen fada a cutar ta Corona da kuma karuwar masu kamuwa da ita, yana mai kara yin kira ga ‘yan kasa da su taka rawa wajen dakile cutar.
A yau Asabar adadin wadanda cutar ta kashe sun kai 374.
342/